Kotu ta aike da matasa gidan yari bisa zargin su da soka wa Yahaya Yahaya wuƙa a Kano

Kotun majistret mai lamba 24 da ke zaman ta a filin tashi da saukar jiragen sama na Mallam Aminu Kano, ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Muttaka Abba Ɗandago, ta aike da wasu matasa gidan gyaran hali bisa zargin su da dukan Yahaya Yahaya da gorori, tare da soka masa wuka a baya lamarin da yake ci gaba da samun kulawar likitoci.
Tunda fari dai ‘yan sandan Kano ne suka gurfanar da matasan a gaban kotun bisa zargin su da hada baki da kuma sanadin rauni da tayar da hankalin al’umma, laifin da suka musanta a gaban kotun.
Hari la yau, zargin ya ayyana cewa, bayan da matasan suka rufe Yahaya Yahaya da duka ne wani matashi mai suna Hassan Danjuma ya soka masa wuka wanda yanzu haka yake kwance a asibiti yana karbar magani.
A yayin zaman kotun na yau Laraba 8 ga watan Afrilu, 2026, wani lauya ya gabata inda ya roki kotun da ta bayar da matasan a beli kasancewar yanzu haka suna tattaunawa a tsakanin bangarorin ‘yan shari’a kuma sulhu ma ya yi nisa.
Kotun ta dage zaman shari’ar zuwa nan da sati biyu domin bayyana matsayar ta a kan batun bayar da belin domin gujewa abinda ka iya zuwa ya dawo.
Wakilinmu Yusif Nadabo Isma’il ya rawaito cewa, mai shari’ar ya kuma bukaci da a zo da mara lafiyar idan har za a iya zuwa da shi gaban kotun domin a ga yanayin jikin nasa



