Kotu ta yanke wa wanda ya bai wa ɗan Adai-daita sahu guba a Kunu, ya sace masa Babur, hukuncin ɗauri da biyan tara a Kano

Kotun Majistiri mai lamba 44 da ke Normansland a Kano, ƙarƙashin jagorancin mai shariʼa, Alhaji Isa Alhaji, ta yanke wa Abdullahi Isah hukunci kan bai wa wani ɗan adaidaita sahu guba a kunun aya, sannan ya sace masa babur ɗin sa.
Tunda fari rundunar ’yan sanda ce ta gurfanar da wanda aka yanke wa hukuncin a gaban kotun, inda aka tuhume shi da laifin haɗa kai, da amfani da guba da kuma satar babur.
Lauyar gwamnati mai gabatar da ƙara, Barrista Rufaida Auwal Mu’alim ta nemi a karanta masa tuhume-tuhumen, inda daga bisani ya amsa laifukan a kotun.
Kotun ta yanke masa hukuncin shekara guda a laifin hada kai ba tare da zabin tara ba, da kuma shekara guda a laifin amfani da guba, kamar yadda kafar Arewa updates ta ruwaito.
Kazalika, kotun ta kuma umurce shi da ya biya kuɗin baburin da ya sace aƙalla naira miliyan uku da dubu dari takwas da saba’in, ko kuma ya shafe shekaru uku a gidan gyaran hali.
Har ila yau, kotun ta kuma gargaɗi wanda aka yanke wa hukuncin da ya zama mutum na gari.



