Sheikh Abduljabbar ya shigar da sabon ƙorafi gaban kotun ɗaukaka ƙara

Fitaccen malamin nan a birnin Kano, Sheikh Abduljabbar Sheikh Nasir Kabara, wanda ke tsare a gidan gyaran hali na Kuje da ke Abuja, ya sake miƙa wata sabuwar takardar ƙorafi zuwa ga Kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a Kano (Kano Division).
Malamin ya shigar da wannan ƙorafi ne sakamakon wani sako da ya ce ya samu daga hannun Shugaban Sashin Shari’a (H.O.D Litigation) na kotun ta wayar tarho a ranar 31 ga watan Maris, 2026, inda aka sanar da shi cewa kotun za ta aika masa da sanarwar ranar zama (Hearing Notice).
Abubuwan da takardar ta ƙunsa;
A cikin takardar mai shafuka biyar, wadda wakilan kwamitin shaidunsa (Eye-witnesses committee) suka miƙa wa kotun a ranar Talata, 7 ga Afrilu, 2026, Sheikh Abduljabbar ya bayyana damuwarsa kan yadda shari’ar ke tafiya.
Manyan ƙorafe-ƙorafensa sun haɗa da:
Batun Sauya Kurkuku: Malamin ya koka kan yadda aka canja masa wurin tsarewa daga Kurmawa da ke Kano zuwa Kuje da ke Abuja a ranar 14 ga Oktoba, 2025, ba tare da barinsa ya kwashi muhimman takardunsa na shari’a ba.
Akwai kuma rashin Takardun Shari'a: Ya bayyana cewa ya shafe watanni biyar bai san halin da takardunsa suke ciki ba, kuma mahukuntan gidan yarin ba su ba shi damar duba su ba yayin da ake shirin mayar da shi Abuja.
Sai kuma haƙƙn Kare Kai: Ya dogara da sashi na 36 (6) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na shekarar 1999 (kamar yadda aka yi wa gyara), wajen neman kotu ta ba shi damar tsayawa ya kare kansa da kansa.
Bukatun Sheikh Abduljabbar;
Daga karshe, malamin ya bukaci Kotun Daukaka Kara da ta amince masa da abubuwa guda uku kafin a ci gaba da sauraron karar:
Ciki akwai mayar da shi gidan gyaran hali na Kurmawa da ke Kano domin ya tantance halin da takardunsa suke ciki, idan an samu wasu daga cikin takardun sun bace ko an sauya su, a ba shi damar maido da su yadda suke.
Kazalika malamin ya tabbatar da cewa takardunsa suna nan daram, sannan kotu ta ba shi sanarwar ranar zama (Hearing Notice) da kuma takardar sammaci (Warrant) na halartar zaman kotun don gabatar da hujjojinsa (Adoption).
Sheikh Abduljabbar ya karkare takardar tasa da cewa tunda aka tsare shi a ranar 16 ga Yuli, 2021, bai taba aikata wani laifi ba, kuma yana rokon kotun da ta duba lamarinsa cikin adalci.
Tashar Dala FM Kano, ta ruwaito cewa, sai dai zuwa lokacin hada wannan rahoton, kotun ba ta riga ta ba da wata sanarwa a kan wannan sabon korafi ba.



