An sake gabatar da waɗanda ake zargi kashe uwa da ƴaƴanta 6 a Kotu a Kano
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Babbar kotun jiha mai zaman ta a Bompai a Kano, ta fara sauraron shari'ar matasan nan da ake zargin su da laifin haɗa baki da kashe wata mata da ƴaƴan ta 6 a gidan Kwari da ke yankin Chiranci Ɗorayi.
Gwamnatin jihar Kano ta kuma tuhumi matasan da laifin kashe uwar gida da amarya, ta hanyar ƙone su da wuta a unguwar Tudun Yola, bayan kashe su.
An kuma zarge su da laifin kashe wata ƙaramar yarinya bayan sun yi mata Fyaɗe, a Shekar mai ɗaki da ke yankin Sabuwar Gansu.
A yayin zaman kotun na ranar Laraba 1 ga watan Apir, 2026, matasan sun musanta zarge-zargen, sai dai Umar Auwal ya amsa laifinsa.
Kotun ta sanya ranar 27 ga wannan wata na 2026, domin fara sauraron shaidu a ƙunshin zarge-zargen da ake yi musu.



