Kotu ta umarci a kamo shugaban jam'iyyar PDP Kabiru Turaki
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin kama tsohon Ministan Ayyuka na Musamman, kuma shugaban jam'iyyar PDP, Tanimu Turaki (SAN), bayan ya ƙi halartar zaman kotu da aka shirya gurfanar da shi.
Rahotanni sun bayyana cewa, kotun ta fusata ne bayan Turaki ya gaza bayyana duk da cewa an sanar da shi ranar zaman shari’ar.
Alkalin kotun ya bayyana cewa babu wani uzuri da zai hana a kamo shi, inda nan take ya bada umarnin a cafke shi tare da kawo shi gaban kotun.
Rahotanni sun bayyana cewa a na zargin Turaki, ne da bayar da bayanan ƙarya ga ‘yan sanda a wata shari’a da ta shafi wani ƙorafi da aka shigar tun a shekarar 2022.
Kotun ta kuma ɗage shari’ar zuwa wani lokaci domin jiran a kamo Turaki, domin a ci gaba da shari'ar.



