Koma Labarai
Shari'a

Lauyoyin gwamnatin Kano ku baiwa kwamishinan shari'a haɗin kai ya zo ne ya yi gyara - AA Haruna Ayagi

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Lauyoyin gwamnatin Kano ku baiwa kwamishinan shari'a haɗin kai ya zo ne ya yi gyara - AA Haruna Ayagi

Shugaban kungiyar kare hakkin ɗan adam ta Human Right Network of Nigeria, Kwamared AA Haruna Ayagi, ya bayyana yajin aikin lauyoyin gwamnatin Kano, a matsayin wani lamari da zai tauye haƙƙin ƴan Shari'a.

AA Haruna Ayagi, ya bayyana hakan ne a yayin zantawar sa da tashar Dala FM Kano, a ranar Talata 24 ga watan Maris, 2026.

Ya ce tattaunawa da mahukunta domin samo bakin zare shi ne mafita maimakon tsunduma yajin aiki.

A cewar sa, "Samun Barrister Abdulkarim Maude SAN, a matsayin kwamishinan shari'a na jihar Kano, ba ƙaramar nasara ba ce, duba da yadda yake ƙoƙari wajen kawo sauyi a fagen shari'a a jihar, in ji shi.”

Kwamared AA Ayagi, ya bayyana cewar Abdulkarim Maude SAN, mutum ne mai jajircewa kuma sun gamsu da yadda yake gudanar da aiki domin haka akwai buƙatar a bashi haɗin kai don samun nasara a aikin.

A kwanakin baya ne dai lauyoyin gwamnati reshen jahar (ano, suka shiga yajin aiki a kan wasu korafe-korafe ciki har da na albashi, sai dai Ayagi ya ce dukkannin matsalolin da suke bayyana wa kwamishinan ya gaje su ne kuma ta hanyar hadin kai ne za a warware su.

Ready to PlayDala FM88.5 FM