Koma Labarai
Shari'a

An gabatar da takardun tuhuma a kan matasan da ake zargi da kashe uwa da ƴaƴanta 6 da wasu laifuka a Kano

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
An gabatar da takardun tuhuma a kan matasan da ake zargi da kashe uwa da ƴaƴanta 6 da wasu laifuka a Kano

Gwamnatin jihar Kano ta gabatar da takardun tuhuma a gaban kotun majistret ta Noman'sland dangane da batun zargin kisan uwa da yayanta 6 a Gidan Kwari da ke yankin Chiranci Ɗorayi.

Da yake bayani a gaban kotun, babban sakatare a ma'aikatar Shari'a ta jihar Kano, Barrister Salisu Muhammad Tahir, ya bayyana wa kotun cewar tuni su ka kammala bincike kuma har sun rubuta takaddar tuhuma a kan matasan da ake zargi domin gabatar da su a kotu mai hurumi.

An dai gurfanar da Umar Auwal, Yakubu Ɗayyabau, Isyaku Yakubu da kuma Umar Ali, a gaban kotun bisa zargin su da laifin haɗa baki da kisan kai a gidan Kwari da ke yankin Chiranci Ɗorayi a ƙaramar hukumar Kumbotso da ke Kano.

Ƙunshin zargin ya bayyana cewar ana zargin matasan sun haɗa baki sun aikata laifin kashe mutane a ungunni daban-daban domin aikata tsafi.

Cikin waɗanda ake zargin sun kashe hadda wata mata da yayan ta 6 a unguwar Chiranci Ɗorayi, da kuma wata mata da abokiyar zamanta a unguwar Tudun Yola, sai kuma wata ƙaramar yarinya da aka zargin cewar sun yi mata Fyaɗe sun kuma cire mata idanu kana suka yanka ta har ta mutu.

Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma'il ya ruwaito cewar, lauyoyin gwamnati sun bayyana wa kotun cewar tuni su ka kammala rubuta tuhume-tuhume domin gurfanar da matasan a gaban babbar kotun jihar Kano.

Ready to PlayDala FM88.5 FM