Koma Labarai
Shari'a

Yajin aikin lauyoyin gwamnati: An ci gaba da shari'a a kotunan Noman'sland a Kano

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Yajin aikin lauyoyin gwamnati: An ci gaba da shari'a a kotunan Noman'sland a Kano

Rahotanni sun bayyana cewa ana ci gaba da shari'a a kotunan majistret na Noman'sland duk da yajin aikin lauyoyin gwamnatin Kano.

Da safiyar yau Laraba dai lauyoyin sun je sun sanya alamar da ta ke nuna cewar ba za ayi aiki a kotunan ba, amma kuma kasancewar akwai alƙalai da ma'aikatan kotuna waɗanda su kuma ba sa cikin yajin aikin hakan bai dakatar da aiki a kotunan ba.

Lauyoyin gwamnatin dai su ne masu gabatar da ƙara a gaban kotuna.

Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma'il ya ruwaito cewa, ƙungiyar lauyoyin gwamnatin jihar Kano, sun tsunduma yajin aikin ne da wannan rana ta Laraba 11 ga watan Maris, 2026, sakamakon rashin biyan su wasu haƙƙoƙinsu da suka ce doka ta ce a biya su.

Ready to PlayDala FM88.5 FM