Koma Labarai
Shari'a

Kotu za ta sanar da ranar yanke hukunci a kan amaryar da ake zargi da kashe mijin ta a Kano

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Kotu za ta sanar da ranar yanke hukunci a kan amaryar da ake zargi da kashe mijin ta a Kano

Babbar kotun jihar Kano mai lamba 14 ƙarƙashin jagorancin mai shari'a Maryam Ahmad Sabo, ta kammala sauraron shaidu a ƙunshin wata shari'a wadda gwamnatin jaha ta shigar tana karar wata mata mai suna Sauda Jibrin Farawa, da zargin kashe mijin ta Salisu Idris Ɗan larai.

Ƙunshin zargin ya bayyana cewar, Saudat wadda amarya ce a wajen Salisu Ɗan larai, ana zargin ta da laifin kashe shi ta hanyar soka masa wuka a wuya a Kano.

Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma'il ya ruwaito cewa, lauyan gwamnati Lamido Soron Ɗinki, ya gabatar da shaidu biyu wanda ya bayyana cewa ya kammala gabatar da shaidun.

Sai dai wadda ake tuhumar ta kare kanta, inda kotun ta sanya wannan rana ta yau dan gabatar da jawabin karshe kafin hukunci.

Ready to PlayDala FM88.5 FM