Mutumin da ake zargi da tuhume-tuhume 10 ciki har da satar daidaita sahu ya samu gurbin zama a gidan yari a Kano
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Kotun majistret mai lamba 44 da ke zamanta a Noman's land a Kano, ta aike da wani mutum gidan gyaran hali bisa zargin sa da satar baburan adaidaita sahu, da kuma laifin baiwa matuƙan adaidaita sahun maganin Bacci.
Tunda fari Ƴan Sanda ne suka gurfanar da mutumin da takardun tuhuma guda 10 dukkansu na zargin satar babur.
Ana zargin mutumin ne da laifin ɗaukar shatar adaidaita sahu da zarar an yi nisa sai ya barbaɗawa direban banju daga nan sai hankali ya ɗauke shi kuma sai ya yi awon gaba da babur ɗin.
Mutumin mai suna Abubakar Sidi Sharif ya musanta dukkan zarge-zargen da ake yi masa a kotun.
Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma'il ya ruwaito cewa, kotun ta aike da mutumin gidan gyaran hali har zuwa ranar 29 ga wannan watan domin jin shaidu.



