Kotu ta bada belin mutanen da su ka ci zarafin Farfesa Umar Sani Fagge

Rahotanni sun bayyana cewa kotun majistare mai lamba 53 da ke zamanta a Norman’s Land, Kano, ta bayaer da belin wasu mutane uku da ake zargi da cin zarafin fitaccen malamin addinin musuluncin nan Sheikh Farfesa Umar Sani Fagge.
An gurfanar da Adamu Adamu da Salihu Bala, da kuma Hassan Umar a gaban alƙalin kotun, Mustapha Sa’ad Datti bisa tuhume-tuhumen da su ka haɗar da haɗin baki domin aikata laifi da cin zarafi da kuma tada tarzoma.
Ana zarginsu da yin kalaman ɓatanci a wani taron siyasa a Kwaciri inda a taron wani Isyaku Mai Fenti ya ce, Akuyar Kwaciri ta fi Malam Umar Sani Fagge, kuma ya wallafa bayanin a shafinsa.
Sai dai ana zargin shi Isyaku Mai Fenti ya gudu.
A yayin zaman kotun a ranar Alhamis 9 ga watan Afrilu, 2026, alƙalin kotun ya saurari karar inda waɗanda ake zargin su ka musanta tuhume-tuhumen.
Daga bisani ne lauyansu ya nemi a bada belin su, inda ta amince da bayar da belin kan sharaɗin naira dubu hamsin ga kowanne daga cikinsu, tare da samar da masu tsaya musu biyu, ɗaya darakta, ɗayan kuma malamin jami’a.
Kotun ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 28 ga watan Afrilu, 2026 domin ci gaba da shari’ar.



