Koma Labarai
Labarai

Majalisar dokokin Kano ta yi Allah wadai da kalaman ɗan majalisar Nasarawa Eng. Yusuf Bello Aliyu.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Majalisar dokokin Kano ta yi Allah wadai da kalaman ɗan majalisar Nasarawa Eng. Yusuf Bello Aliyu.

Majalisar dokokin jihar Kano ta yi Allah wadai da abinda ɗan majalisar Nassarawa Injiniya Yusuf Bello Aliyu ya yi, a baya-bayan nan.

An dai hango ɗan majalisar yana riƙe da kunnuwan zomo tare da ɗaga shi sama tare da faɗin maganganu marasa daɗi.

Ɗan majalisar Minjibir, Abdulhamid Abdul Minjibir ne ya gabatar da ƙudurin gaggawa kan batun tare da kiran majalisar da ta miƙa batun ga kwamitin ladabtarwa don ya kira dan majalisar tare da ɗaukar mataki a kan sa.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM