Hukumar kashe gobara ta ceto Sadiq Ahmad daga ƙasan katangar da ta faɗa masa a Ƙofar mata, Kano.

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano, ta tabbatar da ceto wani matashi mai suna Sadiq Ahmad, daga cikin Katangar da ta faɗa kansa lokacin da suke aikin rusau a unguwar Ƙofar Mata Zango da ke ƙaramar hukumar Birnin Kano.
Jami'in hulɗa da jama'a na hukumar, ACFO Saminu Yusuf Abdullahi, ne ya sanar da hakan ga gidan rediyon Dala FM Kano, a ranar Lahadi 19 ga Yuli, 2026.
Saminu Yusuf Abdullahi ya ce tunda fari sashen karɓar kiran gaggawa na hukumar ta karɓi kira ne daga wani mai suna Naziru Ahmad, inda ya sanar da su faruwar lamarin, a Lahadin nan.
A cewar sa, "Daga isar jami'an mu ne suka tarar wani gini da ake rusau a Kofar mata, ya danne wani mai suna Sadik Ahmad, inda nan take suka ciro shi a raye, tare da kai shi Asibitin Ƙwararru na Murtala Muhammed da ke birnin Kano".
Yusuf ya kuma ce bayan da likitoci suka bashi kulawar gaggawa ne jami'ansu suka miƙa shi zuwa ga hannun ɗan uwan sa Nazir Ahmad, domin ci gaba da kula da shi.
Ya ce sun kan bincike domin gano musabbabun faruwar Iftila'in, domin har yanzu ba su tabbatar da ainihin dalilin da ya haifar da hakan ba.
Sanarwar ta kuma ce, Daraktan hukumar kashe gobarar ta ƙasa reshen jihar Kano, Alhaji Sani Anas, ya kuma ja hankalin al'umma da su rinƙa kulawa a yayin da suke rushe gine-gine, ko yin sabon gini, domin gujewa faruwar abinda ka iya zuwa ya dawo.



