Koma Labarai
Labarai

Majalisa ta buƙaci gwamnatin Kano ta gaggauta kai wa al'ummar Bichi ɗauki kan rasa rayuka da dukiyoyi bisa fuskantar Iftila'in iska da ruwan sama.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Majalisa ta buƙaci gwamnatin Kano ta gaggauta kai wa al'ummar Bichi ɗauki kan rasa rayuka da dukiyoyi bisa fuskantar Iftila'in iska da ruwan sama.

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta bukaci gwamnatin jihar da ta gaggauta kai dauki ga al'ummar Karamar Hukumar Bichi da ambaliyar iska da ruwan sama ta shafa, inda mutane takwas suka rasa rayukansu, yayin da gidaje da dukiyoyi da dama suka lalace.

Bukatar ta fito ne bayan ɗan majalisar mai wakiltar ƙaramar hukumar Bichi, Lawan Shehu, ya gabatar da kudirin gaggawa a zaman majalisar da shugaban Majalisar, Jibril Ismail Falgore, ya jagoranta.

Lawan Shehu ya ce bala'in da ya afku a ranar Alhamis din da ta gabata ya yi sanadin mutuwar mutane takwas tare da lalata gidaje da dukiyoyin da darajarsu ta kai miliyoyin naira.

Ya kara da cewa shi tare da Shugaban Karamar Hukumar Bichi sun ziyarci yankunan da abin ya shafa domin jajanta wa iyalan mamatan da kuma duba irin barnar da aka yi.

Dan majalisar ya kuma yi kira ga gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf da ta samar da kayan agajin gaggawa da sauran tallafin da za su taimaka wa wadanda wannan ibtila'i ya shafa.

Wakilinmu na majalisar dokokin jihar Kano Sunusi Shu'aibu Musa ya ruwaito cewa, Bayan muhawara kan kudirin, Majalisar ta amince da shi baki ɗaya tare da buƙatar gwamnatin jihar ta hanzarta kai agaji da tallafin da ya dace ga dukkan waɗanda abin ya shafa.

Ready to PlayDala FM88.5 FM