Koma Labarai
Labarai

An naɗa Usman Abdullahi (Liman Oil) a matsayin Sarkin Kasuwar Sabon titin Fanshekara, Kano.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
An naɗa Usman Abdullahi (Liman Oil) a matsayin Sarkin Kasuwar Sabon titin Fanshekara, Kano.

Hakimin Kumbotso, kuma Barden Kano, Alhaji Abdullahi Lamiɗo Sanusi, ya naɗa Usman Abdullahi wanda akasafi sani da Liman Oil, a matsayin Sarkin Kasuwar Sabon Titin Fanshekara.

Hakimin ya naɗa Usman Abdullahi wanda akafi sani da Liman Oil, a matsayin Sarkin Kasuwar Sabon titin Fanshekara, ne ranar Laraba 16 ga Satumba, 2026, a fadarsa, a wani mataki da aka bayyana a matsayin naɗin farko na irin wannan matsayi a kasuwar.

Da yake jawabi jim kaɗan bayan naɗin, Hakimin Kumbotso, kuma Barden Kano, Alhaji Abdullahi Lamiɗo Sanusi, ya hori sabon Sarkin Kasuwar Sabon titin Fanshekara, Mallam Usman Abdullahi Liman, da ya mayar da hankali wajen ci gaban kasuwar, tare da sanya ido kan tsaro da kuma yaƙi da ɓata gari.

Ya kuma buƙaci Sarkin Kasuwar ya tsawatar wa dukkanin masu bayyana batsa a yayin tallan magunguna a kasuwar.

Shima a nasa ɓangaren, Sarkin Kasuwar Sabon titin Fanshekara, Mallam Usman Abdullahi wanda aka fi sani da Liman Oil, ya bayyana wa Dala FM Kano, cewa, a shirye yake wajen samar da ci gaban da ya dace a kasuwar.

A cewar sa, "Za mu zauna da dukkan ƴan kasuwar domin duba a kan yadda za mu kawo ci gaban da ya dace a tsakanin ƴan kasuwar ta ɓangarori daban-daban," in ji Liman.

Ya kuma ce, zai yi duk mai yiyuwa wajen magance matsalolin tsaro, da yaƙi da masu yaɗa batsa a tallan magungunan gargajiya, da sauran su.

A yayin taron naɗin, Sarkin Kasuwar Sabon titin Fanshekara Mallam Usman Abdullahi Liman, ya samu rakiyar shugabannin ƙungiyar kasuwar, da ƴan kasuwar da dama, da ma jami'an tsaro daban-daban.

Ready to PlayDala FM88.5 FM