Koma Labarai
Tsaro

Mutumin da ake zargi da surfawa dagaci zagi ya shiga hannun rundunar Kossap a Kano

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Mutumin da ake zargi da surfawa dagaci zagi ya shiga hannun rundunar Kossap a Kano

Rundunar tsaro da ke yaƙi da faɗan daba da ƙwacen waya da kuma daƙile ta'ammali da kayan maye, ta Anti-Phone Snatching Force a Kano, ta kama Musa Shu'aibu Maƙeri, bisa zargin sa da cin mutuncin dagacin Shekar Mai Ɗaki Mallam Badamasi Abdulƙadir.

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar tsaron Ibrahim Garba Ahmad, ne ya bayyana hakan a zantawar sa da Dala FM Kano a ranar Alhamis 30 ga watan Afrilu, 2026.

Ya ce bayan da suka samu ƙorafi kan cin mutuncin dagacin da mutumin ya yi ne, kwamandan rundunar Nura Salisu Sharaɗa, ya tura jami'an sa inda suka kamo shi tare da faɗaɗa bincike.

Ibrahim Garba Ahmad ya kuma ce, akwai abin takaici kan yadda mutumin ya rinƙa surfawa dagacin ashariya ba tare da ya yi masa komai ba, duk kuwa da kima da darajar da yake da ita a garin na Shekar Mai Ɗaki da ke Kano.

Da yake jawabi dagacin garin Shekar Mai Ɗaki Mallam Badamasi Abdulƙadir, ya ce Musa Maƙeri, ya daɗe yana cin mutuncin sa ba tare da ya yi masa komai ba, a don haka ne ɗauki gaɓarar miƙa koken sa ga rundunar Anti-Phone Snatching Force Kano, domin bi masa haƙƙinsa.

"Mun haɗu da yaron a wajen mai sana'ar POS, ya rinƙa cin mutunci na ta yadda na ga dama, na ƙyale shi na wuce amma duk da haka sai da ya biyo ni a kan Keke yana cin zarafi na dukka ban tanka masa ba, in ji Dagacin.”

Da yake bayyana nadamar sa mutumin da ake zargi Musa Shu'aibu Maƙeri, ya ce ya gane kuskuren sa dangane da cin mutuncin da ya yi wa dagacin inda ya buƙaci da ya yi haƙuri ba zai sake aikata irin hakan ba.

Daga ƙarshe Kakakin rundunar tsaron ta Anti-Phone Snatching Force da ke Kano, Ibrahim Garba Ahmad, ya ce da zarar sun kammala bincike za a miƙa mutumin inda ya dace domin girbar abinda ya shuka.

Ready to PlayDala FM88.5 FM