Al’ummar gari sun ƙone mutane uku da ransu kan kisan basarake a Filato.

Rahotanni sun bayyana cewa wasu fusatattun mutanen gari a yankin ƙaramar hukumar Lagntan ta Arewa da ke jihar Filato, sun cinna wa mutane uku wuta kan zargin su da kashe basaraken yankin Ƙwallon, mai riƙe da sarautar Ponzi Kwallak,
Majiyoyin labarin sun ce fusatattun mutanen sun cinna wa mutanen wuta ne a ranar Juma'a 24 ga watan Afrilu, 2026, bayan da waɗanda aka ƙona ɗin sun kai hari a gidan basaraken a cikin daren Alhamis.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa, ’yan fashin sun kuma sace baburin basaraken da wayarsa, bayan sun kashe shi, lamarin da ya harzuƙa al’ummar yankin suka shiga farautar su.
"Dubun ’yan fashin ta cika ne a lokacin da suke ƙoƙarin sayar da baburin da suka sace, kuma bayan an titsiye su, sun amsa laifin da ake zargin su da aikatawa a nan ne aka ƙaddamar musu, in ji shaidun."
Wasu mazauna yankin sun yi ƙoƙarin miƙa su ga jami’an tsaro, amma wasu fusatattu suka fi ƙarfinsu, suka ƙwace waɗanda ake zargin suka cinna musu wuta har lahira a kusa da Sakatariyar Ƙaramar Hukumar Lagntan ta Arewa ta jihar Filato.
Kafar yaɗa labarai ta Aminiya ta ruwaito cewa ta yi ƙoƙarin jin ta bakin ’yan sandan jihar Filato dangane da lamarin, amma abin ya ci tura.



