Koma Labarai
Tsaro

Mun kama matasan da suka ƙwaci wayar da aka aika Yara kai caji - KOSSAP a Kano

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Mun kama matasan da suka ƙwaci wayar da aka aika Yara kai caji - KOSSAP a Kano

Rundunar tsaro da ke yaki da fadan daba da kwacen waya da ta'ammali da kayan maye ta Anti Phone Snaching Force ta jihar Kano, (KOSSAP) ta kama wasu matasa uku bisa zargin su da kwatar wayar wasu yara da aka aike su kai caji a unguwar Jajurma.

Kwamandan rundunar a Kano Nura Salisu Sharada, ne ya bayyana kama matasan uku yayin zantawar sa da gidan rediyon Dala FM, a Talatar nan, ya ce bayan da suka samu korafi a kan aika-aikar da matasan su biyar suka yi ne ya tura jami'an su inda suka kamo uku daga cikin su.

A cewar sa, "Matasan da mu ka kama sun bayyana mana cewa suna sana'ar gyaran babura, da su ka je wucewa ne daya daga cikin su ya kwaci wayar kuma suka gudu daga bisani mu ka kamo uku daga cikin su, in ji shi."

Nura Salisu Sharada, ya kuma ce da zarar sun kammala bincike za su dauki mataki a kan matasan da ake zargi da aika-aikar, inda ya kuma yi kira ga iyaye da su kara kula da tarbiyyar ya'yansu domin gujewa aikata laifin da za su zo su na yin dana sani.

Biyu daga cikin matasan da aka kama masu suna Sa'idu Musa Hassan, da Adamu Kabir, sun ce bayan da aka kama su da aka caje su aka samu wayar da suka kwata a jikin sa, amma sun yi nadama ba za su sake aikata irin wannan laifin ba.

Daga bisani dai kwamandan rundunar ta Anti-Phone Sanching Force a Kano, Nura Salisu Sharada, ya kuma gargadi masu aikata irin wannan laifi da su daina domin duk wanda suka kama ba zai ji da dadi ba.

Ready to PlayDala FM88.5 FM