Koma Labarai
Tsaro

Lokaci ya yi da ƴan majalisar tarayya za su ɗauki nauyin kare rayukan ƴan Najeriya - Human Rights

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Lokaci ya yi da ƴan majalisar tarayya za su ɗauki nauyin kare rayukan ƴan Najeriya - Human Rights

Ƙungiyar Center for Human Rights and Charity Development Initiatives, ta bayyana damuwarta da kuma fushi kan yadda kashe-kashen jama’a da hare-haren tashin hankali ke ƙara tsananta a sassa daban-daban na yankin Arewa.

Babban daraktan ƙungiyar a Najeriya, Kwamared Dr. Auwal Jibril Maifada, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya aikowa Dala FM Kano, a ranar Lahadi 5 ga watan Afrilu, 2026.

A cewar sa, "A yau al’ummomi da dama suna rayuwa a cikin rashin tsoro da rashin tabbas, bisa yadda kusan kowace rana ake samun rahotannin kashe-kashen jama’a, garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa, da kuma hare-haren da ke tilastawa iyalai da dama barin gidajensu, in ji shi.”

Ya kuma ce waɗannan matsalolin da ake fuskanta a sassan arewacin Najeriya lamarin ya zama babbar barazana ga zaman lafiya, tsaro da kuma makomar ƙasar.

A cewar Dr. Maifada, abin da ya fi tayar da hankali shi ne yadda aka ga kamar shiru da sakaci daga wasu daga cikin shugabannin da al’umma suka zaba domin wakiltarsu a zauren majalisar dokokin ƙasar, duk da irin wannan mummunan yanayi da kasa ke ciki, har yanzu ba a ga matakan gaggawa da suka dace daga yawancin sanatoci da ƴan majalisar wakilai ba.

Ƙungiyar ta kuma ce haƙƙin ƴan majalisa bai tsaya kawai a kan tattaunawar siyasa ko amfani da muƙami ba, domin kuwa kundin tsarin mulkin Najeriya ya ɗora musu nauyin kare jin daɗin jama’a, tabbatar da tsaro da kuma sa ido kan ayyukan gwamnati.* Idan aka ci gaba da yin shiru a lokacin da rayukan jama’a ke salwanta, hakan na iya zama babbar gazawa wajen sauke amanar da aka ba su.

Maifada ya kuma yi kira ga dukkan ƴan Majalisar Tarayya da su tashi tsaye su nuna cewa sun cancanci amanar da al’umma suka ba su, domin lokaci ya yi da za a daina siyasar anmani da muƙami, a mayar da hankali kan kare rayukan jama’a.

Ready to PlayDala FM88.5 FM