Koma Labarai
Tsaro

Tun da shekarar 2026 ta zo ban ji labarin samun fadan daba tsakanin ungwanni a Kano ba - Kwamishinan 'Yan Sanda

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Tun da shekarar 2026 ta zo ban ji labarin samun fadan daba tsakanin ungwanni a Kano ba - Kwamishinan 'Yan Sanda

Kwamishinan 'yan sandan jihar Kano CP Ibrahim Adamu Bakori, ya ce tun da aka shigo wannan shekara ta 2026, bai ji labarin an samu wani fadan daba a tsakanin unguwanni ba a sassan jihar Kano, sakamakon tashi tsaye da aka yi wajen magance matsalar.

CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bayyana hakan ne ta cikin shirin Dan Sanda da jama'a na gidan rediyon Dala FM Kano, da ya gudana a ranar Talata 31 ga watan Maris, 2026.

Wannan na zuwa ne a yayin Makon 'Yan Sanda da aka fara gudanar wa daga ranar Litinin, a wani bangare na ranar 'Yan Sanda, ta kasa da za a gudanar a ranar 7 ga watan Apir, 2026.

Ya kuma ce rundunar tana bakin kokarin ta wajen dakile harkokin fadan daba, da kwacen waya, da kuma sauran laifuka a fadin jihar.

A cewar sa, ''Mu na buƙatar al'umma ku kara ba mu hadin kai wajen rinka hanzarin sanar da jami'an mu faruwar wani al'amari da ka iya kawo tazgaro a harkar tsaro, domin dakile faruwar wata matsala cikin sauri, in ji shi."

CP Bakori, ya kuma ce za a hukunta dukkanin jami'in su da aka samu da laifin karbar kudi beli, kasancewar doka ta hana karbar kudin belin domin kyauta ne.

Ya kuma yaba da irin gudunmawar da al'umma suke bai wa rundunar, inda ya buƙaci jama'a su rinƙa sanar da rundunar duk abinda ka iya kawo matsalar tsaro ta lambobin waya Kamar haka, 08032419754, ko 09029292926, ko kuma 08123821575.

Ready to PlayDala FM88.5 FM