Koma Labarai
Tsaro

Shugaba Tinubu ya yi Allah-wadai da kashe rayuka a birnin Jos da jihar Kaduna

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Shugaba Tinubu ya yi Allah-wadai da kashe rayuka a birnin Jos da jihar Kaduna

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya yi Allah-wadai da kakkausar murya dangane da hare-haren rashin imani da wasu ‘yan bindiga suka kai a gundumar Angwan Rukuba da ke Jos, ta Jihar Filato, da kuma ƙauyen Kahir da ke Ƙaramar Hukumar Kagarko a Jihar Kaduna.

Shugaban ya bayyana waɗannan hare-hare, waɗanda suka haɗa da kisan jama’a a Jos da kuma garkuwa da baki ’yan bikin aure a Kaduna, a matsayin babban kalubale ga hadin kan Najeriya.

Ya kuma tabbatar wa ‘yan kasa cewa ba za a zura ido wadanda suka aikata wannan danyen aikin su sha da dadi ba.

A cikin wata sanarwa da Mai Magana da Yawun Shugaban Kasa kan fannin Yada Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Talata, Shugaba Tinubu ya bayyana maharan a matsayin azzalamai kuma matsorata.

"Duk wanda zai fake da duhun dare ya kashe mutanen da ba su da kariya kamar yadda aka yi a Jos da ƙauyen Kahir, to matsoraci ne marar tausayi. Manufar waɗannan maharan ita ce su haifar da ramuwar gayya domin jini ya ci gaba da kwarara," in ji Shugaban.

Shugaba Tinubu ya ba wa jami’an tsaro umarnin su kara kaimi wajen kamo wadanda suka aikata laifin da kuma wadanda ke yada labaran karya da nufin ruruta wutar rikici. Haka kuma, ya ja kunnen wasu bangarorin kafafen yada labarai da ke kokarin danganta hare-haren da batun addini.

Babban matakin da Shugaban ya dauka sun hada da:

Kiran Jami'an Tsaro: Ya bukaci jami'an tsaro su rika amfani da bayanan sirri don dakile hare-hare kafin su auku.

Ceton Waɗanda Aka Sace: Ya ba da umarnin gaggauta ceto sauran mutanen da aka yi garkuwa da su a kauyen Kahir.

*Kayayyakin Aiki* Ya bayyana cewa gwamnati na kan hanyar sayo manyan makaman zamani don bin sawun miyagun mutane a duk inda suke.

Shugaban ya jinjina wa Gwamna Caleb Mutfwang na Jihar Filato da Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna bisa kokarinsu na shawo kan lamarin da kuma tallafawa ayyukan ceto.

Daga ƙarshe, ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalai da suka rasa rayukansu, sannan ya yi addu’ar samun sauki ga wadanda suka jikkata, yana mai kira ga al’umma da su ba wa jami’an tsaro hadin kai don tabbatar da zaman lafiya.

Ready to PlayDala FM88.5 FM