Koma Labarai
Tsaro

Gwamnati a ja matasa a jiki don yaƙi da faɗan daba, ƙwacen waya da shan kayan maye - Gamayyar Matasan Kano

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Gwamnati a ja matasa a jiki don yaƙi da faɗan daba, ƙwacen waya da shan kayan maye - Gamayyar Matasan Kano

Ƙungiyar Gamayyar Matasan Kano ta ce matukar ana son a kawo ƙarshen rikicin faɗan daba, da ƙwacen waya, da ta'ammali da kayan maye a jihar nan, sai gwamnati da al'umma sun ƙara jan matasa a jiki wajen magance musu abubuwan da ke damun su.

Shugaban Ƙungiyar Gamayyar Matasan Kano, Muhammad Tijjani Ɗorayi (MTD) ne ya bayyana hakan a zantawar sa da Dala FM, a ranar Alhamis 26 ga Maris, 2026.

Ya ce sun lura da cewa rashin aikin yi, da ƙarancin ilimi, da kuma rashin jan matasan a jiki domin jin damuwar su, wajen magance musu, na taka rawa wajen ƙara ta'azzarar faɗan daba da ƙwacen waya, da shaye-shayen kayan maye a tsakanin matasan.

A cewar sa, "Indai za a rinƙa jan matasan mu a jiki, tare da jin damuwar su ana kuma magance musu su, babu makawa za a cire musu sha'awar daba, ƙwacen waya, da shaye-shayen kayan maye a zuciyar su, in ji shi.”

Muhammad Tijjani MTD, ya kuma buƙaci ƴan siyasa su cire hannun su daga karɓo ɓata garin da ake kama wa wajen aikata laifuka, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen daƙile ƙalubalen tada hankalin al'umma a sassan jihar.

MTD, ya kuma shawarci matasa da su tashi tsaye wajen kama sana'a da za su rinƙa dogaro da kansu, tare da yin watsi da dukkan abubuwan da basu kamata ba domin tsira da mutumcin su.

Ready to PlayDala FM88.5 FM