A gaggauta binciken harin sojoji da ya kashe fararen hula a Yobe da Borno - Human Rights

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Center for Human Rights and Charity Development Initiatives, ta yi Allah wadai, tare da nuna tsananin fushi kan rahotannin kisan fararen hula da rundunar sojojin saman Najeriya ta aikata a Jihar Yobe, da Borno.
Daraktan ƙungiyar a Najeriya Dr. Auwal Jibril Maifada, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwar manema labarai da ya aikowa Dala FM Kano, a ranar Laraba 15 ga Afrilu, 2026.
A cewar sa, wannan lamari mai matuƙar muni da rashin amincewa ya nuna babban take haƙƙin ɗan adam, musamman hakkin rayuwa kamar yadda yake ƙunshe a Sashe na 33 na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya na shekarar 1999 (da aka yi wa kwaskwarima), da kuma wasu dokokin kare hakkin dan Adam na kasa da kasa da Najeriya ta amince da su.
A ranar Asabar 11 ga watan Afrilu, 2026, ne dai sojojin saman suka kai harin a kasuwar Jilli da ke ƙaramar hukumar Geidam ta jihar Yobe, ana tsaka da cin kasuwa lamarin da ya yi sanadiyyar rasuwar gomman mutane, inda jami'an su ka ce an kai wa fararen hular harin ne bisa kuskure.
"Muna matuƙar damuwa cewa fararen hula maza, mata da yara su ne ke ci gaba da zama waɗanda ke shan wahala a irin waɗannan hare haren soji wanda ya kamata su kare su, in ji shi."
Ya ci gaba da cewa, maimaita irin waɗannan kura-kurai na janyo tambayoyi masu yawa dangane da yadda ake gudanar da ayyukan soji, da rashin ɗaukar alhaki, da kuma nuna halin ko in kula wajen kare rayukan fararen hula.
Ƙungiyar ta CHRCDI, ta kuma yi Allah wadai da ƙarfi ga rundunar sojojin saman Najeriya kan wannan sakaci da ya jawo asarar rayukan marasa laifi.
Dr. Auwal Maifada, ya kuma yi kira da a gaggauta gudanar da bincike mai zaman kansa, da gaskiya da adalci, domin gano waɗanda ke da hannu tare da hukunta su.
Ya kuma buƙaci da a biya diyya ga iyalan waɗanda lamarin ya shafa bisa tanadin dokokin kasa da na duniya.
"Mu na kira da a sake duba tsarin gudanar da hare haren soji, domin tabbatar da bin dokokin yaƙi na ƙasa da ƙasa da kuma kare fararen hula, in ji Dr. Auwal."
A cewar Maifada, rashin ɗaukar matakin gaggawa kan wannan lamari zai kara rage amincewar jama’a ga gwamnati da hukumomin tsaro.



