Ƴan bindiga sun sace zaɓaɓɓen shugaban ƙaramar hukuma

Rahotanni sun bayyana cewa wasu ƴan bindiga sun sace zaɓaɓɓen shugaban ƙaramar hukumar Sapele ta jihar Delta, Chief Bright Abeke, da yammacin ranar Juma’a da misalin ƙarfe 7 a wani otel.
Shaidun gani da ido sun shaidawa jaridar Punch cewa, wasu ‘yan bindiga kusan 15 ne suka kai harin, inda su ka riƙa harbi domin tsoratar da mutane kafin su ɗauke shugaban ƙaramar hukumar zuwa wani wuri da ba a sani ba har yanzu.
Majiyoyin sun ce a yayin harin, an harbi wani ɗan sa-kai mai suna Ufuoma, wanda rahotanni suka bayyana cewa an garzaya da shi asibiti domin samun kulawar likitoci.
A cewar shaidar, bayan faruwar lamarin, jami’an tsaro sun kulle hanyoyin shiga da fita a Sapele, kuma ‘yan sanda sun fara aiki domin ceto shugaban ba tare da lahani ba, tare da shan alwashin kama waɗanda suka sace shi, kamar yadda kafar Daily Nigerian Hausa ta ruwaito.



