Shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin jihar Zamfara ya tsallake rijiya da baya daga harin ƴan bindiga
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Shugaban ma'aikata na fadar gwamnatin jihar Zamfara Alhaji Moukhtar Lugga, ya tsallake rijiya da baya a yammacin jiya Alhamis da misalin karfe 6:16.
Wasu 'yan bindiga dauke da makamai ne dai su ka buɗe wa motarsa wuta a hanyar Funtua zuwa Gusau a daidai Kucheri.
Rahotanni sun bayyana cewa ƴan bindigar sun kewaye ta kowane ɓangare na motar, inda su ka buɗe mata wuta, sai dai cikin ikon Allah duk harsasan da aka harba ba su samu direban motar ba, lamarin da ya basu damar guduwa.
An dai hango wata babbar ɓula a gilashin gaban motar da harsashi ya yi a jiki, al'amarin da aka ƙara yi wa Moukhtar da direban sam Barka bisa yadda harsasai suka gaza samun su.



