Matashin da ya yi wa mai unguwa zagin tsamar nama ya shiga hannun Kossap a Kano

Rundunar tsaro da ke yaki da fadan daba da ƙwacen waya da ta'ammali da kayan maye ta Anti Phone Snaching Force da ke nan Kano, ta kama wani matashi Usman Musa Tautau, bisa zargin sa da zagin Jarman Shekar Mai daki, kuma Mai unguwar Bubbugaje Jajurma da ke karamar hukumar Kumbotso, Zakiru Musa.
Mai magana da yawun rundunar a Kano, Ibrahim Garba Ahmad, ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da gidan rediyon Dala FM Kano a ranar Alhamis 2 ga watan Afrilu, 2026.
Ya ce bayan samun korafi a kan zagin da matashin ya yi wa mai unguwar ne kwamandan rundunar Nura Salisu Sharada, ya umarci OC Zaman lafiya na rundunar Abdullahi Garba Soja, inda ya jagoranci tawaga har su ka kamo matashin.
Ibrahim Garba ya kuma gargadi dukanin masu niyyar aikata irin wannan laifi da su daina kasancewar ba za su saurara wa duk bata garin da suka kama da aikata laifi ba.
Da yake zantawa da gidan rediyon Dala FM, matashin da ake zargi da zagin mai unguwar, Usman Musa Tautau, ya ce sharrin kwaya ce ta sa shi zagin mai unguwar, daga daga yanzu ya yi bankwana da kwayar.
Daga bisani dai mai magana da yawun rundunar tsaron ta Anti Phone Snaching Force a nan Kano, Ibarahim Garba Ahmad, ya kuma gargadi matasan da ke tada hankalin jama'a da su daina kasancewar duk wanda ya fada komar su ba zai ji da dadi ba.



