Koma Labarai
Tsaro

Buɗaɗɗiyar wasiƙa zuwa ga gwamnan Kano a kan shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa Ogan Ɓoye.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Buɗaɗɗiyar wasiƙa zuwa ga gwamnan Kano a kan shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa Ogan Ɓoye.

Wani ɗan gwagwarmaya Ayman Ado Usman, ya aike da buɗaɗɗiyar wasiƙa zuwa ga gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, kan faruwar wani al'amari game da shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa Yusuf Imam (Ogan Ɓoye).

A cikin buɗaɗɗiyar wasiƙar da Ayman Ado, ya wallafa a shafin sa na Facebook, domin ganin ta je ga gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa;

Hotunan da ke ƙasa an ɗauke su ne a jiya yayin tarɓar da aka yi wa guda daga cikin yan gaban goshin gwamnan Kano, wato shugaban karamar hukumar Nassarawa Yusuf Imam, (Ogan Ɓoye) bayan dawowarsa daga Ibadar Umarah.

A cewar Ayman, a hakan fa wai ibadar Umarah, ya je ba wai dawo wa ya yi daga taron Gangi ko farautar shekara ba.

A cikin hotunan an hango tarin matasa riƙe da muggan makamai, da Gorori, a hannun su, a gaban motocin sa, suna ɗaga su sama, tamkar za a tafi farauta ko kuma an dawo.

A cewar Ayman, muddin Gwamna Abba Kabir Yusuf bai tsawatar wa Ogan Ɓoye ba, to tabbas babu komai a cikin ajandar "KANO FIRST" ta gwamna Abba sai Propagandar siyasa, da wasa da hankalin mutanen Kano.

Ko a shafukan sada zumunta na irin su Facebook, an hango yadda al'umma suka rinƙa ɗora hotunan tare da kira ga gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, da ya ɗauki mataki kan faruwar lamarin domin ƙarfafa harkar tsaro da ceto rayuwar matasa.

A ranar Asabar 28 ga watan Maris, 2026, ne dai shugaban ƙaramar hukumar ta Nassarawa Yusuf Imam (Ogan Ɓoye) ya dawo daga ibadar Umrah, inda aka hangi tarin matasa sun yo masa rakiya ɗauke da muggan makamai da kuma Gorori a hannunsu, al'amarin da ya tayar da hankalin al'umma.

Ready to PlayDala FM88.5 FM