Koma Labarai
Tsaro

Hisbah ta musanta kama shugaban ƙaramar hukuma a Kano

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Hisbah ta musanta kama shugaban ƙaramar hukuma a Kano

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta musanta labarin da wasu suke yaɗa wa cewar ta kama shugaban wata ƙaramar hukuma da wasu makusantansa suna aikata baɗala wani hotel a jihar.

Mataimakin babban kwamandan hukumar, kan al'amuran yau da kullum Dakta Mujahideen Aminuddin Abubakar, ne ya sanar da hakan a zantawar sa da gidan rediyon Dala FM, a ranar Alhamis 26 ga watan Maris, 2026.

Ya ce akwai shugaban wata ƙaramar hukuma a Kano, da ya ga maza da mata suna abinda bai kamata ba a cikin wani ruwa, inda ya bada gudummawa har aka kama su, a wani ɓangare na daƙile alfasha.

A cewar sa, "Bayan ɓullar labarin ne wasu suka juya labarin tare da yaɗa labari mara tushe balle maka da sunan neman "Tranding" wanda hakan kuskure ne, in ji shi."

Wannan na zuwa ne bayan da hukumar Hisbah ta jihar Kano ta cafke mata 11 masu ƙananan shekaru, da kuma wasu matasa 10, da ake zargin su da aikata baɗala a wani Hotel, da ke yankin Kureƙen Sani a Kano.

Ready to PlayDala FM88.5 FM