Kotu ta soke nasarar Abdullahi Basaf tare da ayyana Ali Musa Hard worker a matsayin shugaban ƙaramar hukumar Kumbotso

Babbar Kotun jiha mai lamaba 17 karakashin mai shari'a Abdu Mai Wada Abubakar, ta soke nasarar Abdullahi Basaf a matsayin shugaban karamar hukumar Kumbotso da ke jihar Kano.
Kotun ta kuma tabbatar da Ali Musa Ɗanmaliki (Hardwoker), a matsayin shugaban ƙaramar hukumar Kumbotso.
Wannan na cikin umarnin kotun da ta ɓulla a ranar Talata 24 ga watan Maris, 2026, bayan da aka dade ana Shari'a a kai.
Kazalika, kotun ta ayyana cewa, takardar da hukumar zaɓe ta jihar Kano ta bai wa Basaf, haramtacciyar ce.
Kotun ta kuma umarci wanda ake kara na uku, hukumar zaɓe ta KANSIEC, da ta gaggauta baiwa mai ƙara Ali Musa Danmaliki, takardar shaidar cin zaɓe.
Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma'il ya ruwaito cewa, har ila yau, kotun ta kuma ayyana cewar bin wannan umarnin ya zama wajibi a wajen gwamnatin jihar Kano.



