Koma Labarai
Tsaro

Mun kama masu ƙwacen waya da sayar da ƙwayoyi a filin idin Kwakwa - Ƙungiyar Gyara Kayan ka a Kano

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Mun kama masu ƙwacen waya da sayar da ƙwayoyi a filin idin Kwakwa - Ƙungiyar Gyara Kayan ka a Kano

Gamayyar ƙungiyar Gyara Kayan ka ta jihar Kano, ta ce jami'an ta sun kama aƙalla matasa 8 da zargin sayar da ƙwayoyi, da masu ƙwacen waya ɗauke da muggan makamai a filin idin Kwakwa da ke garin Zawachiki a ƙaramar hukumar Kumbotso, Kano.

Mataimakin shugaban Gamayyar ƙungiyar a Kano, kuma shugaban ta a ƙaramar hukumar Kumbotso, Sagir Sa'idu Zawaciki, ne ya shaida wa Dala FM Kano, hakan a yammacin ranar Juma'a 20 ga Maris, 2026.

Ya ce sun kama matasan ne a cikin filin idin Kwakwar a dai-dai lokacin da su ke sintiri haɗin gwiwa da rukunin jami'an tsaro, domin ƙarfafa tsaro a cikin filin, wajen ganin an gudanar da shagalin Sallar lafiya a yankin.

A duk lokacin ranar ƙaramar sallah da babba dai al'umma, maza da mata, samari da ƴan mata, da kuma yara da dama ne suke yin cikar ɗango zuwa filin idin da yammacin ranar sallah, domin sada zumunci, da kuma sayen kayan ƙwalam da maƙulashe a cikin filin.

A cewar Sagir Zawaciki, "Binciken su ya gano musu cewar da yawan matasan da suka kama sun shiga cikin filin idin Kwakwar ne domin ƙwatar wayar jama'a, da sayar da ƙwayoyi, yayin da wani matashin ma burin ya shi ne ya ketawa mata haddi a filin, in ji shi.“

Ya kuma ce tuni suka miƙa matasan inda ya dace domin ganin an ɗauki mataki na gaba a kan su, domin hakan ya zama izina ga sauran matasa masu niyyar aikata irin hakan.

Ya kuma buƙaci al'umma musamman ma matasa da su ƙara kwaɗaituwa da zama mutanen kirki bayan kammala azumin watan Ramadan, tare da zama mutanen kirki kamar yadda aka ji faɗakar wa a lokacin azumin.

Ready to PlayDala FM88.5 FM