Koma Labarai
Tsaro

Civil Defense ta cafke mutane 6 kan zargin lalata ƙarfen digar jirgin ƙasa a Kano

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Civil Defense ta cafke mutane 6 kan zargin lalata ƙarfen digar jirgin ƙasa a Kano

Rundunar tsaron Civil Defence a Jihar Kano, ta cafke wasu mutane shida da ake zargi da lalata ƙarfen digar jirgin kasa a Karamar Hukumar Kiru ta jihar.

Kwamandan rundunar na Jihar Kano, Mohammed Hassan Agalama ne ya bayyana hakan yayin ganawar sa da manema labarai a ranar Laraba 18 ga Maris, 2026.

A cewar sa, "Jami’an mu sun kama Sulaiman Salisu mai shekaru 45, da Musa Aliyu Harisu mai shekaru 22, sai Ishaq Alhassan mai shekaru 20, Isa Aminu mai shekaru 35, Sadiq Bala mai shekaru 20 da Mansur Idris mai shekaru 22, dukkaninsu ’yan asalin Jihar Kaduna, in ji shi.”

Ya kuma ce an kama mutanen ne bayan samun bayanan sirri da kuma sintiri, inda aka same su suna lalata ƙarfen digar jirgin kasa, tare da kwato wasu sassa da kayan da suke amfani da su wajen aikata laifin.

Ready to PlayDala FM88.5 FM