Jami'an mu ku ƙarfafa tsaro yayin bikin ƙaramar sallah a Kano - Ƙungiyar Bijilante

Ƙungiyar sintirin Bijilante ta jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Ubale Muhammad Barau Badawa, ta buƙaci dukkanin jami'an ta a faɗin jihar, da su halarci masallatan Idi domin bayar da tsaro, don ganin an gudanar da sallar lafiya.
Jami'in hulɗa da jama'a na ƙungiyar a Kano, kuma kwamandan ta a Fagge, Usman Muhammad Ɗandaji, ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da Dala FM Kano, a ranar Laraba 18 ga watan Maris, 2026.
Wannan na zuwa ne a dai dai lokacin da ake ci gaba da shirye-shiryen bukuwan ƙaramar sallar wadda za a gudanar a gobe Alhamis ko kuma Juma'a, da ke tafe.
Usman Ɗandaji, ya ce kwamandan ƙungiyar Bijilanten na jihar Kano, Ubale Barau Muhammad Badawa, ya kuma umarci dukkanin ƴan ƙungiyar da su halarci dukkan inda suka san ana bukuwan sallah, domin samar da tsaro don ganin an gudanar komai lafiya.
A cewar sa, "Mun baza jami'an mu lungu da saƙo na Kano, domin ganin an ƙara ƙarfafa tsaro a yayin bukuwan ƙaramar sallar, in ji Ɗandaji.”
Wannan na zuwa ne yayin da ake shirin gudanar da bikin ƙaramar sallar idi, a gobe Alhamis, ko kuma Juma'a, wanda tuni fadar mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar na uku, ta buƙaci a fara duban jinjirin watan Shawwal daga yau Laraba 18 ga Maris, 2026.



