Koma Labarai
Tsaro

Rundunar Anti-Phone Snatching Force ta kama matashin da ke murɗewa Zakaran mutane wuya a Kano

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Rundunar Anti-Phone Snatching Force ta kama matashin da ke murɗewa Zakaran mutane wuya a Kano

Rundunar tsaro da ke yaƙi da faɗan daba da ƙwacen waya da kuma ta'ammali da kayan maye, ta Anti-Phone Snatching Force a nan Kano, ta kama wani matashi Abdullahi Ibrahim, bisa zarginsa da yi wa yara wayo ya karɓe wayar da aka aike su kai caji, tare da murɗewa Zakaran mutane Wuya a unguwar Sheka Ɗanfodiyo.

Kwamandan rundunar tsaron a nan Kano, Nura Salisu Sharaɗa, ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da Dala FM Kano, jim kaɗan da kama matashin, ya ce sun ramu rahoto kan abinda matashin ya aikata inda ya tura jami'an su suka je suka kamo shi.

A cewar sa, "Binciken mu ya gano cewa sai matashin ya yi shaye-shayen sannan yake zuwa yana murɗewa Zakara, ko Kazar mutane wuya, idan ya kama a yankin Sheka, sannan ya je ya gasa domin ya ci, kuma za mu ɗauki matakin da ya dace a kan sa, in ji shi.”

A nasa ɓangaren matashin da ake zargi da ƙwacen wayoyi da kuma murɗewa Zakara ko Kazar mutane wuya a cikin unguwa, Abdullahi Ibrahim, ya ce aƙalla ya haura shekara uku yana aikata aika-aikatar, amma dai ya yi nadama ba zai ƙara aikata irin hakan ba.

Daga bisani dai, kwamandan rundunar tsaron ta Anti-Phone Snatching Force da ke nan Kano, Nura Salisu Sharaɗa, ya buƙaci matasa masu niyyar aikata ire-iren wannan laifi da su daina domin ba za su saurara wa duk wanda ya shigo komar su ba.

Ready to PlayDala FM88.5 FM