Haɗakar jami'an tsaro sun daƙile hare-haren ƴan Boko Haram a Maiduguri da Damboa cikin dare

Rahotanni sun bayyana cewa, haɗin gwiwar jami’an tsaro sun daƙile wasu hare-haren da ake zargin ’yan ta’addar Boko Haram sun kai a yankin Ajilari Cross - Kofa a Maiduguri da kuma Karamar Hukumar Damboa ta Jihar Borno.
Ƴan ta'addan dai sun yi yunƙurin kai hare-haren ne a cikin daren wayewar Litinin 16 ga Maris 2026 wanda ya yi daidai da 27 Ramadan, 1447.
Hakan na cikin sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno, ASP Nahum Kenneth Daso, ya fitar a ranar Litinin 16 ga Maris 2026.
Sanarwar ta nuna cewa jami’an tsaro sun isa yankin Ajilari Cross zuwa Kofa domin duba halin da ake ciki tare da ɗaukar matakan da suka dace bayan rahoton wani hari da aka daƙile a yankin.
A wani lamari na daban kuma a Karamar Hukumar Damboa, jami’an tsaro sun dakile wani hari da aka kai da misalin ƙarfe 1 na dare, inda daga bisani aka dawo da zaman lafiya.
Tashar rediyon Dandalkura da ke Maiduguri ta rawaito cewa, jiragen saman Sojin ƙasar nan sun kai ɗauki yayin da aka ji ƙarar harbe-harben bindiga a wasu sassa na birnin Maiduguri, lamarin da ya janyo firgici a tsakanin wasu mazauna yankunan kafin daga bisani lamarin ya lafa baki ɗaya.



