Koma Labarai
Tsaro

Matasa ku daina bari ana amfani da ku wajen tada hankalin al'umma - Gamayyar Matasan Kano

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Matasa ku daina bari ana amfani da ku wajen tada hankalin al'umma - Gamayyar Matasan Kano

Ƙungiyar gamayyar matasan Kano, ta yi kira ga al'ummar jihar da na Ɗorayi, da su ƙara dagewa wajen yi wa jihar addu'a a cikin wannan wata na Ramadan, domin ƙara samun zaman lafiya da ma daƙile matsalar tsaro.

Shugaban gamayyar matasan Muhammad Tijiani Ɗorayi (MTD) ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da gidan rediyon Dala FM Kano, biyo bayan ɗage taron shan ruwan da suka gabatar wa duk shekara a ranar 25 ga watan Ramadan na kowacce Shekara.

Ya kuma ce a ƙa'ida suna shirya taron shan ruwan ne tare da ƴan kwamitin tsaron yankin Ɗorayi, na Mashal 116, da kuma masu taimaka musu 50, domin sanya su farin ciki bisa ƙoƙarin da suke yi wajen yaƙi da matsalar tsaro a yankin da ma jihar Kano baki ɗaya.

A cewar sa, "Mu na kira ga gwamnatin Kano, da ma al'ummar jihar, da su ƙara jan matasa a jiki domin kawar musu da harkokin faɗan daba, ƙwacen waya, da ta'ammali da kayan maye, a faɗin jihar, in ji shi.”

Ya kuma shawarci matasa da su kaucewa barin ana amfani da su wajen tada hankalin al'umma musamman ma a wannan lokaci na watan azumin Ramadan.

Muhammad Tijiani Ɗorayi, ya kuma bayyana jin daɗi da godiya ga hukumomin tsaro da ma'aikatun gwamanati, bisa turo wakilicin da suka yi domin halartar taron shan ruwan, duk kuwa da bayyana ɗage shi bisa bayanan da aka samu na matsalar tsaro, yana mai cewa nan gaba kaɗan za a shirya wani taron.

Sai dai MTD, ya sake yin kira ga gwamnan jihar Kano da ya basu dama domin ƙungiyar gamayyar matasan Kano, ta gana dashi bisa ɗumbin shawarwarin da suke da su a gare shi kan matsalar tsaron da ake fuskanta a wasu sassan Kano.

Ready to PlayDala FM88.5 FM