Al'ummar Tukuntawa a Kano, na alhinin mummunan kisan gillar da aka yi wa ɗan kwamitin tsaron yankin Usaini Bashir Sabo.

Al’ummar unguwar Tukuntawa da ke Kano, na cikin alhini kan mummunan kisan gillar da wasu ’yan daba suka yi wa wani matashi ɗan kwamitin tsaron yankin Usaini Bashir Sabo, a ranar Juma’a 6 ga watan Maris, 2026.
A cikin sanarwar da shugaban kwamitin tsaron yankin Auwal Garba Soja ya fitar, a madadin kwamitin tsaron yankin Tukuntawa, ya bayyana cewa marigayin na daga cikin matasan da ke taimakawa wajen kula da tsaron al’umma domin daƙile ayyukan ɓata gari a unguwar.
ʼYan daban sun yi wa matashin mummunan sara a tsakiyar kansa, abin da ya raba kansa gida biyu.
Tuni Majalisar Matasa ta ƙasa reshen jihar Kano ta nemi Gwamnati ta gaggauta ɗaukar matakai game da lamarin
A wata sanarwa da Shugaban majalisar na Jihar Kano Hassan Garba Abdullahi ya aikawa jaridar Arewa Updates, ya nuna damuwa game da kisan gillar.
Majalisar ta kuma ba da shawarar kafa ofishin ’yan sanda a unguwar Tukuntawa musamman a bayan gidan namun dajin Kano wato Gidan Zoo domin kara karfafa tsaro da daƙile ayyukan ’yan daba.



