Ramadan: Duk mai kunnen ƙashin da mu ka kama da laifi yayin fita sallar dare zai fuskanci hukunci - Bijilante a Kano

Rundunar yan sintirin Bijilante ta jihar Kano, ta Jaddada aniyar ta na sanya ƙafar wando ɗaya ga dukkan wani ɓata garin da ke amfani da lokacin Sallar dare ta Tahajjudi, su ke satar kayan jama'a tare da ƙwacen wayoyin mutane.
Tashar Dala FM Kano, ta ruwaito cewa, Babban Kwamandan rundunar a Kano Alhaji Shehu Muhammad Rabi'u, ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da manema labarai a ranar Talata 10 ga watan Maris, 2026.
Ya ce yanzu haka jami'an Bijilanten sama da dubu 6,700, wasu da kayan sarki wasu kuma da fararen kaya ne ke aiki a loko da sakunan Unguwannin Kano, domin tabbatar da inganta harkokin tsaron rayuka da dukiyoyin al'ummar jihar a lokacin watan azumin nan na Ramadan.
Shehu Rabi'u, ya kuma ja hankalin iyaye da su tabbatar sun kula da duk wani motsin 'yayan su, domin gudun shiga hurumin hukumomin tsaro, wanda hakan ka iya haifar musu da matsala.
Ya kuma ce duk mai kunnen ƙashin da suka kama da laifi zai girbi abinda ya shuka, domin kuwa za su miƙa shi ga hukumar da ta dace don ɗaukar mataki na gaba a kansa.



