Koma Labarai
Tsaro

Gwamnatin Najeriya, ta san inda duk wani Ɗanbinda ya ke a ƙasar - Sheikh Gumi

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Gwamnatin Najeriya, ta san inda duk wani Ɗanbinda ya ke a ƙasar - Sheikh Gumi

Fitaccen malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Abubakar Gumi, ya yi iƙirarin cewa gwamnatin ƙasar ta san sunaye da kuma duk guraren da ‘yan ta’adda su ke a cikin ƙasar.

Malamin ya yi wannan zargi ne yayin da ya ke magana a wata hira da ya yi da kafar DRTV, wadda ta fara yaɗuwa sosai a yau Talata.

Gumi na mayar da martani ne ga maganganun da ake cewa shi da kansa ya san tare da hulɗa da ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane har kuma ya na mu'amala da su ko kare su.

Jaridar The Punch ta rawaito cewa, a cewar Sheikh Gumi, mu'amala da yake yi da waɗannan ƴan ta'addan ba shi kaɗai ya ke yi ba, sai da ya haɗa da jami’an tsaro.

Ready to PlayDala FM88.5 FM