Ramadan: Mun ba za zaratan jami'an mu a guraren ibada domin samar da tsaro a Kano - Anti-Phone Snatching Force

Rundunar tsaro da ke yaƙi da faɗan daba, ƙwacen waya da kuma daƙile ta'ammali da kayan maye, ta Anti-Phone Snatching Force a Kano, ta gargaɗi dukkanin ɓata garin da ke yunƙurin ƙwacen wayoyin jama'a a cikin dare yayin zuwa sallar dare ta Tuhajjudi.
Kwamandan rundunar tsaron a Kano, Nura Salisu Sharaɗa, ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da gidan rediyon Dala FM Kano, a ranar Laraba 11 ga watan Maris, 2026.
Ya ce yanzu haka sun tura zaratan jami'an su lungu da saƙo a cikin dare a faɗin jihar, domin kare rayuka da kuma dukiyoyin al'umma a cikin kwanakin ƙarshe na watan azumin Ramadana.
A cewar sa, "Babu ɗaga ƙafa tsakanin mu da dukkanin ɓata garin da ke kitsa faɗan daba, ƙwatar wa mutane waya, ko satar musu kayayyaki a gidajen su, duk wanda muka kama sai ya yi dana sani, in ji shi.”
Nura Sharaɗa, ya kuma ce yanzu haka sun tura zaƙaƙuran jami'an su a guraren da ake yin ibada, musamman ma sallar dare ta Tuhajjudi, domin tabbatar da tsaron al'umma.
"Duk wanda ya ce ba za a zauna lafiya ba a faɗa masa shi ne ba zai zauna lafiya, domin duk inda aka samu matsalar tsaro kan kace kwabo jami'an mu na KOSSAP Damisa Ƙi Sabo, za su je domin ba da agajin gaggawa, in shi Nura.”
Ya kuma buƙaci al'umma da su rinƙa hanzarin sanar da su dukkan wani ɓakon al'amari musamman ma na faɗan daba, ƙwacen waya, ko shaye-shaye, da dillancin kayan maye, ta lambar waya kamar haka 08166157799, domin kawo musu ɗauki.



