Koma Labarai
Tsaro

Ɓarayin daji sun kashe mutane 15 a jihar Katsina da tsakar rana

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Ɓarayin daji sun kashe mutane 15 a jihar Katsina da tsakar rana

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a ƙauyukan Falale da Kadobe na karamar hukumar Jibia, ta jihar Katsina, a ranar Talatar nan 17 ga Maris, 2026.

Kazalika, lamarin ya faru ne tsakanin 'yan sintiri da wasu tubabbun ‘yan bindiga, kamar yadda kafar DCL Hausa ta ruwaito.

Jihar Katsina, dai na daga cikin jahohin Arewa da ke fama da matsalar hare-haren ƴan ta'adda masu garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa, ko da ike gwamnatin jihar, da jami'an tsaro na ci gaba da ƙoƙari domin magance matsalar.

Ready to PlayDala FM88.5 FM