Koma Labarai
Tsaro

Ƴan bindiga sun kashe daraktan kwalejin ilimi bayan karɓar kuɗin fansa Miliyan 25.7 da Babura a Zamfara

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Ƴan bindiga sun kashe daraktan kwalejin ilimi bayan karɓar kuɗin fansa Miliyan 25.7 da Babura a Zamfara

Wasu da ake zargin ’yanbindiga ne sun kashe Malam Bashar Sani, wani babban jami’in gudanarwa a Kwalejin Ilimi ta Maru a Jihar Zamfara, duk da cewa iyalansa sun biya kuɗin fansa masu yawa domin a sako shi.

Binciken da kafar yaɗa labarai ta PRNigeria ta gudanar ya nuna cewa, marigayin ya kashe akalla naira miliyan 25.7 wajen biyan fansa da wasu buƙatun ’yan bindiga domin ceto ’yan uwansa da aka sace a lokuta daban-daban, kafin daga bisani su kashe shi.

Majiyoyi daga dangin mamacin da al’umma sun bayyana cewa hare-haren ’yanbindiga kan iyalan Bashar Sani sun fara ne tun shekarun da suka gabata, lokacin da suka sace matansa biyu daga gidansa da ke Tsohon Tasha a ƙaramar hukumar Maru. Domin a sake su, an ce ya biya naira miliyan biyu.

Sai dai kuma bayan watanni kaɗan, ’yan bindigar sun sake dawowa suka sace ƙaninsa Hassan Sani, wanda shi ma aka sako bayan an biya naira miliyan 3.5, tare da miƙa musu katinan caji da wayoyin hannu kamar yadda suka buƙata a lokacin.

Kazalika, Saboda yawan hare-haren, marigayin ya tilasta komawa da iyalansa wani gida kusa da ’yan uwansu a unguwar Shiyyar ’Yan Hudu a garin Maru domin neman tsaro.

Hassan Sani ya ce sun samu ɗan kwanciyar hankali na kusan watanni 18, kafin ’yan bindigar su gano sabon wurin zamansu suka kai wani sabon harin a lokacin.

A wannan farmakin, ’yan bindigar sun sace Bashar Sani, ɗaya daga cikin matansa da aka taɓa sacewa a baya, da kuma ’yarsa, tare da wasu mazauna yankin. Haka kuma an kashe matar wani ɗan sanda yayin da aka sace ’ya’yanta biyar.

’Yan bindigar sun nemi naira miliyan 20 domin sakin su, inda iyalin suka biya kuɗin gaba ɗaya, tare da ƙarin buƙatu kamar babura, katinan caji na naira dubu 200 da wayoyi huɗu.

Daga baya maharan sun sake ƙara buƙatar babura 15, amma bayan tattaunawa aka rage zuwa babura uku, wanda iyalan suka saya suka miƙa wa ƴan bindigar.

Sai dai bayan an miƙa su, ’yan bindigar sun umarci iyalan su koma gida su jira saƙo game da sakin waɗanda aka sace.

Hassan Sani ya ce daga baya suka gano cewa an riga an kashe ɗan’uwansa a lokacin, lamarin da ya tayar musu da hankali.

Rahotanni sun ce daga baya ’yan bindigar sun umurci iyalan su je ƙauyen Gidan Kano a ƙaramar hukumar Maradun domin karɓar waɗanda aka sako. A can ne suka samu matar marigayin da ’yarsa da sauran mutanen da aka sako, amma Bashar Sani bai kasance tare da su ba.

Matarsa ta bayyana musu cewa ya rasu ne tun yana hannun ’yan bindigar.

Kafar Daily Nigerian Hausa ta ruwaito cewa, bincike ya nuna cewa Bashar Sani ya mutu ne a sansanin ’yan bindigar bayan azabtarwa mai tsanani da kuma matsalolin lafiya, ciki har da karyewar ƙafa da bai samu magani ba.

Ready to PlayDala FM88.5 FM