Mun ba za jami'an mu lungu da saƙo don samar da tsaro yayin bikin sallah a Kano - Anti-Phone Snatching Force

Rundunar tsaro da ke yaƙi da faɗan daba, da ƙwacen waya da kuma ta'ammali da kayan maye, ta Anti-Phone Snatching Force ta jihar Kano, ta ce ta ba za jami'an ta lungu da saƙo na jihar nan domin ƙarfafa tsaro a lokacin bukukuwan sallar idi domin ganin an daƙile shirin ɓata gari.
Kwamandan rundunar a Kano, Nura Salisu Sharaɗa, shi ne ya sanar da hakan a zantawar sa da gidan rediyon Dala FM Kano, lokacin da yake bayyana kaɗan daga shirin da suka yi domin samar da tsaro a yayin bukukuwan sallar.
A cewar sa, "Mun tura jami'an mu na farin kaya, da masu sanye da Kaki, cikin sassan jihar Kano, domin ganin an ɗauki dukkan matakan da suka dace na daƙile matsalar tsaro, don al'umma su gabatar da bikin sallar lafiya, in ji Nura.”
Ya kuma ce duk wanda ya ce jihar Kano ba za ta zauna lafiya ba, to a faɗa masa sai dai idan shi ne ba zai zauna lafiya, bisa yadda suka yi shiri na kawar da ɓata gari a lokacin bikin sallar a sassan jihar.
Nura Sharaɗa, ya kuma buƙaci iyaye da su ja ƴaƴansu a jiki tare da tsawatar musu wajen kaucewa aikata laifi, domin duk ɓata garin da ya faɗa komar su ba za su saurara masa ba.



