Koma Labarai
Tsaro

Raunika 6 ɓata gari suka yi mini a sassan jiki na - Hadimin gwamnan Kano Gamboliya Ja'en

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Raunika 6 ɓata gari suka yi mini a sassan jiki na - Hadimin gwamnan Kano Gamboliya Ja'en

Mai Taimakawa gwamnan Kano kan harkokin yaɗa labarai Hon. Gamboliya Ja'en, ya yi kira ga jami'an tsaro da su zurfafa bincike domin gano waɗanda suka sassare shi a sassan jikinsa domin ɗaukar mataki na gaba.

Gamboliya Ja'en ya shaida wa Dala FM Kano, cewa, a ranar Juma'a 13 ga Maris, 2026, ne wasu ɓata gari suka farmake shi a unguwar Ja'en bayan gidan Katakore bayan Big Trust, a lokacin da ya fito daga cikin motar sa bayan ya dawo daga karɓowa ƴaƴansa kayan sallah.

A cewar sa, "Bayan na fito daga cikin mota ta ne sai kawai na ji an hau ni da sara ta ko ina, daga nan ne ban sake gane abinda ya faru ba sai gani na na yi a asibiti, in ji Gamboliya.”

Ya kuma ce bayan faruwar lamarin gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya shiga cikin lamarin inda aka kai shi zuwa Asibitin ƙwararru na Murtala Muhammed da ke jihar, inda aka ba shi kulawar gaggawa.

Gamboliya Ja'en ya kuma yaba wa Baturen ƴan sandan Sharaɗa CSP Abdulrrahim Adamu, bisa ƙoƙarin da ya yi wajen bashi kula wa a kan lamarin.

A cewar sa, "Aƙalla raunika shida ɓata garin suka yi mini a sassan jiki na, inda aka yi mini ɗinki; Kuma kullum ina faɗa musu rayuwar Gamboliya Ja'en a hannun Allah take ba a hannun wani ba, in ji shi.”

Wakilinmu Abdulƙadir Sani Tukuntawaa Ya ruwaito cewa, Gamboliya ya kuma ce yanzu ya fara gwagwarmaya wajen ci gaba da kare muradan gwamnatin jihar Kano, kuma abinda aka yi masa wani abu ne da aka ƙara masa ƙaimi a kan gwagwarmaya.

Ko a watan Agustan 2025, sai da wasu ɓatagari su ka yi ajalin Babban Mai ɗaukkowa Gwamnan Kano rahoto a Maʼaikatar Tarihi da Alʼadu ta jihar Hon. Sadiq Gentle, a wani hari makamancin wannan.

Ready to PlayDala FM88.5 FM