An samu raguwar matsalar tsaro yayin bikin sallar bana - Anti-Phone Snatching Kano

Rundunar tsaro da ke yaƙi da faɗan daba, ƙwacen waya da ta'ammali da kayan maye, ta Anti-Phone Snatching Force Kano, ta bayyana cewa an samu raguwar matsalar tsaro a yayin sallar idin da aka gudanar ta ƙaramar Sallah, yau a Kano.
Kwamandan rundunar tsaron a jihar, Nura Salisu Sharaɗa, ne ya bayyana wa Dala FM Kano, hakan a ranar Juma'a, lokacin da yake bayyana nasarorin da aka samu bisa ƙarfafa tsaro da aka yi a jihar.
A cewar sa, "An samu nasarar gudanar da sallar idin lafiya ne sakamakon haɗin kan da aka samu daga ɓangaren rukunin jami'an tsaro daban-daban, tare da gudummawar da suka al'umma suka bayar, in ji shi.”
Nura Sharaɗa, ya kuma ja kunnen matasa da su zauna lafiya, yana mai cewa duk wanda ya tada hankalin al'umma a yayin bukukuwan ƙaramar Sallar idan ya shigo komar su ba zai ji da daɗi ba.
"Mun tura jami'an mu duk guraren da ake wasanni, da harkokin nishaɗi a yayin bikin sallar, domin samar da tsaro domin ganin an ƙara wanzar da zaman lafiya a faɗin jihar Kano, a cewar sa.”
Ya ƙara da cewa, rundunar ta KOSSAP, za kuma ta ci gaba da ƙoƙari wajen ganin an gudanar da bukukuwan sallar lafiya, a don haka ya buƙaci iyaye su ja wa ƴaƴansu kunne da su zauna lafiya, domin gujewa fuskantar Matsala.



