Koma Labarai
Tsaro

Na saci wayoyi sama da 20, ta hanyar Sane, ina sayen kayan shaye-shaye - Matashi a Kano

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Na saci wayoyi sama da 20, ta hanyar Sane, ina sayen kayan shaye-shaye - Matashi a Kano

Rundunar tsaro ta Anti-Phone Snatching Force da ke jihar Kano, ta cafke wasu matasa masu ƙananan shekaru da ake zarginsu da Sanen wayoyinsu jama'a a sassan jihar Kano.

Mai magana da yawun rundunar tsaron ta Anti-Phone Snatching Force a nan Kano, Ibrahim Garba Ahmad, ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da Dala FM Kano, a ranar Laraba 25 ga watan Maris, 2026.

Ya ce hakan na zuwa ne biyo bayan ƙorafin da suka samu kan yadda matasan suka addabi yankin gidan Zoo, da Rijiyar Lemo, da kasuwanni da sauran gurare a sassan jihar nan, inda suke amfani da dabarar sayar da ruwan Pure Water, suna sane wayoyin jama'a.

Sai dai Ibrahim Garba ya ce, ko da matasan suka sane wayar wata budurwa ne a yankin gidan Zoo, ne dubunsu ta cika jami'an rundunar ƙarkashin OC Zaman lafiya dole, Abdullahi Soja, suka cafke matasan da bincike ya yi nisa aka gano waya da kuɗin budurwar a wajen su.

Lawisa Nura Hashim, ita ce budurwar da matasan suka sanewa waya da kuɗi daga cikin jakar ta yankin gidan Zoo, ta godewa jami'an rundunar bisa yadda suka ƙwato mata waya da kuɗin nata.

Da yake jawabi guda daga cikin matasan da ake zargin, ya ce zuwa yanzu ya sane wayoyin jama'a kusan guda ashirin, amma wannan shi ne na ƙarshe zai kama sana'a.

A cewar sa, "Daga fara wannan harkar aƙalla na sane wayoyin jama'a sama da guda Ashirin, ina shaye-shayen Tabar Wiwi, da Sigari, da kuma ƙwayoyi, da abinci da kuɗin wayoyin idan na sayar, in ji matashin.”

Daga bisani rundunar tsaron ta Anti-Phone Snatching Force da akafi sani da KOSSAP, ta gargaɗi matasa masu niyyar aikata irin wannan laifi da su daina, domin ba za su saurara wa duk wanda ya shiga hannun su ba.

Ready to PlayDala FM88.5 FM