Koma Labarai
Tsaro

Masu fashin waya sun sake kashe wani mutum a gadar Kawo tare da ɗauke wayar sa

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Masu fashin waya sun sake kashe wani mutum a gadar Kawo tare da ɗauke wayar sa

Rahotanni sun bayyana cewa masu ƙwacen waya sun sake kafa shinge a Gadar Kawo ta jihar Kaduna, tare da kashe wani mutum a gurin.

A cewar shaidun gani da ido, lamarin ya faru ne a daren ranar Asabar lokacin da ɓarayin suka cakawa wani mutum wuka, tare da ƙwace wayarsa, inda nan take rai ya yi halinsa.

“Muna buƙatar ƙarin sintirin ’yan sanda da kuma na’urorin kyamara na sa ido domin kama irin waɗannan barayi,” in ji wani mazaunin yankin.”

Al’ummar da ke yankin sun yi kira ga mahukunta da a ƙara tsaurara matakan tsaro domin hana irin wannan lamari a nan gaba.

Ready to PlayDala FM88.5 FM