Koma Labarai
Tsaro

Matashin da ke canza wa mutane ATM ya kwashe musu kuɗi a asusun banki ya shiga hannun Kossap a Kano

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Matashin da ke canza wa mutane ATM ya kwashe musu kuɗi a asusun banki ya shiga hannun Kossap a Kano

Rundunar tsaro da ke yaƙi da faɗan daba da ƙwacen waya da kuma daƙile shaye-shayen kayan maye, ta Anti-Phone Snatching Force a Kano, ta cafke Muhammad Najib bisa zarginsa da laifin canza wa wani mutum katin cirar kuɗi ATM, a wani gidan Mai, tare da kwashe masa kuɗi Naira dubu 270 a asusun ajiyar bankin sa.

Kwamandan rundunar tsaron ta Anti-Phone Snatching Force a Kano, Nura Salisu Sharaɗa, ne ya bayyana wa Dala FM Kano, kama matashin a ranar Litinin 27 ga Afrilu, 2026.

Ya ce binciken su ya gano cewa matashin ya saba zuwa gidajen Mai, da gurin masu POS, da sauran sana'o'i, yana canza wa mutane katin cirar kuɗi, sannan ya je ya kwashe musu kuɗaɗe ya yi harkokin gaban sa da su.

A cewar Nura, "Yanzu da Muhammad Najib ya canza wa wani mutum katin ATM, ya je ya kwashe masa kuɗi Naira dubu 270, mutumin ya yi ƙorafi jami'an mu suka je suka kamo shi, kuma mu na ci gaba da bincike, in ji shi.”

Da yake bayyana nadamar sa matashi Muhammad Najib, ya ce wannan shi ne karo na farko da aka kama shi kan aika-aikatar da yake yi ta canza wa mutane katin cirar kuɗi a gurare daban-daban, amma ba zai ƙara ba.

Daga bisani dai kwamandan rundunar tsaron ta Anti-Phone Snatching Force Nura Salisu Sharaɗa, ya ce za su miƙa matashin inda ya dace domin ganin sun girbi abinda ya shuka.

Ya kuma gargaɗi matasan da su ke addabar jama'a da harkokin faɗan daba, da ƙwacen waya, da kuma dillanci, da shan kayan maye da su daina, inda ya ce duk wanda suka kama da irin waɗancan zarge-zarge ba za su saurara masa ba, domin ƙara damun zaman lafiya a faɗin jihar Kano.

Ready to PlayDala FM88.5 FM