Koma Labarai
Tsaro

Gwamna sai fa ka saka baƙin glass a kan ƴan siyasar da ke yawo da ƴan daba a Kano - Gamayyar Matasan Kano

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Gwamna sai fa ka saka baƙin glass a kan ƴan siyasar da ke yawo da ƴan daba a Kano - Gamayyar Matasan Kano

Ƙungiyar nan da ke rajin hana faɗan daba da ƙwacen waya da kuma shaye-shaye ta Gamayyar Matasan Kano, ta ce matuƙar ana son gyaruwar tarbiyyar matasa a Kano, sai gwamnatin jihar ta daƙile yawon da ƴan daba a yayin taruka siyasa.

Shugaban ƙungiyar ta Gamayyar Matasan Kano, Muhammad Tijjani Ɗorayi mai laƙabin MTD, ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da gidan rediyon Dala FM a ranar Laraba 29 ga watan Afrilu, 2026.

Ya ce akwai buƙatar gwamnatin Kano ta tsawatar wa ƴan siyasa da su daina amfani da matasa wajen tada hankalin al'umma da makamai, musamman ma a yayin tarukan siyasa a jihar.

A cewar sa, "Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, sai fa ka saka baƙin Glass a kan ƴan siyasar da ke yawo da ƴan daba, domin daƙile kashe rayuka da dukiyoyin al'umma, in ji MTD.”

Ya ce akwai abin takaici kan yadda ƴan siyasa suke yawo da ƴan daba a sassan jihar, al'amarin da ke tada hankalin al'umma tare da asarar dukiyoyi, a wasu lokutan ma har da asarar rayukan mutanen da ba su ji ba kuma ba su gani ba.

Ya kuma yi kira ga gwamna Abba Kabir Yusuf, da a gaggauta naɗa Kwamishinan tsaron cikin gida tare da dawo da tsarin nan na tudun mun tsira domin yaƙi da faɗan daba da ƙwacen waya a tsakanin matasa.

Muhammad Tijjani Ɗorayi, ya kuma buƙaci matasa da su daina bari a yi amfani da su wajen tada hankalin al'umma, duba da yadda hakan ke kassara rayuwar su ta ɓangarori daban-daban.

Ready to PlayDala FM88.5 FM