Dagacin Sharaɗa ya jagoranci taro a kan hanyoyin daƙile faɗan daba da tabbatar da zaman lafiya a yankin.

Dagacin garin Sharaɗa da ke ƙaramar hukumar Birni a Kano, Alhaji Iliyasu Mu'azu Sharaɗa, ya jagoranci wani taron tattaunawa a kan hanyoyin da za a bi domin daƙile matsalolin faɗan daba da tabbatar da zaman lafiya a yankin.
Taron, wanda aka gudanar jiya Laraba, a fadar Dagacin bayan dawowarsa daga aikin Hajji a kasar Saudiyya, ya haɗa da jami’an tsaro da suka haɗar da DSS, baturen ƴan sandan Sharaɗa, sarakunan gargajiya, masu unguwanni, iyayen yara da kuma wasu daga cikin matasan da ake zargi da hannu a rikice-rikicen da suka faru a yankin.
Da yake jawabi a taron, Dagacin Sharada Alhaji Iliyasu Mu'azu Sharaɗa, ya bayyana cewa bayan Makkah da Madina, babu wani gari da ya fi ƙauna kamar Sharada, yana mai cewa ya sadaukar da kansa wajen kare mutunci da martabar yankin da Allah ya dora masa amanarsa.
Dagacin ya kuma gargaɗi matasan da cewa duk wanda aka samu da hannu a fadan daba a nan gaba zai fuskanci hukunci bisa doron doka, ciki har da ɗaurin kurkuku.
A nasa bangaren, Baturen Ƴan Sanda na Sharada, CSP Abdulrahim Adamu, ya yabawa Dagacin bisa wannan mataki na hada masu ruwa da tsaki da ya yi, domin tattauna matsalolin tsaro, yana mai jaddada cewa babu wanda ya fi ƙarfin doka.
Ya kuma yi kira ga matasa da su guji aikata ayyukan da za su ɓata sunan Sharada, wadda ya bayyana a matsayin gari mai cike da zaman lafiya.
A karshen taron, matasan da ake zargi da sauran mahalarta taron sun rattaɓa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya, tare da ɗaukar alƙawarin cewa ba za su sake shiga ko amincewa da aikata fadan daba a yankin Sharada ba.



