Ba za mu lamunci ƴan siyasa su rinƙa tsoma mana baki a kan duk wanda muka kama da hannu a harkar miyagun ƙwayoyi ba a Kano - Barr Muhyi Rimin Gado

Kwamitin Yaƙi da Shaye-shaye da faɗan daba da Gwamnatin jihar Kano ta kafa, ya ce ba zai lamunci ƴan siyasa su rinƙa tsoma masa baki ba a kan gudanar da aikin kwamitin, ko neman a saki waɗanda suka kama da zargin ta'ammali da miyagun ƙwayoyi da daba a jihar.
Shugaban Kwamitin, Barista Muhyi Magaji Rimin Gado, ne ya bayyana hakan a yayin taron masu ruwa da tsaki da Gamayyar Matasan Kano, ta shirya aka gudanar a yankin Ɗorayi a ranar Lahadi 26 ga Yuli, 2026.
Ya kuma ce Gwamnatin Kano za ta ɗauki tsattsauran mataki a kan duk wanda aka samu da hannu harkar dillancin miyagun ƙwayoyi a Kano, tare da tallafawa tsaro a faɗin jihar.
Da yake nasa jawabin, Mai martaba Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sanusi II, ta hannun wakilcin da ya samu na Sarkin Sulluɓawan Kano, kuma Hakimin Gundumar Gwale, Alhaji Idris Sunusi Bayero, ya ce taron da Gamayyar Matasan Kano, suka gudanar sun yi abinda ya dace a irin wannan lokaci.
A nasa jawabin, Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ta hannun wakilcin da ya samu na mataimakinsa mai kula da Shiryyar Estan By Pass, Usman Abdullahi Kamba, ya ce kasancewar shan miyagun ƙwayoyi na taka muhimmiyar rawa wajen haifar da matsalar tsaro a Kano, akwai buƙatar kowa ya sanya hannu don ganin an daƙile dillancin kayan mayen.
Muhammad Tijjani Ɗorayi MTD, shi ne Shugaban Ƙungiyar Gamayyar Matasan Kano, ya ce sun shirya taron ne domin tara masu ruwa da tsaki don wayar da kan matasa a kan illar shaye-shayen kwayoyi, da kuma lalubo hanyoyin magance matsalolin tsaro a Ɗorayi da kewaye.
Shi kuwa shugaban sashen yaƙi da daba na rundunar ƴan sandan Kano, CSP Bashir Gwadabe, cewa ya yi, matasa su tsaya su yi abinda ya dace, idan kuwa suka ki to da su za su gamu.
Taron dai ya samu damar halartar al'umma da dama, kuma ciki har da kama daga ɓangaren Gwamnatin jihar Kano, da Masarautar Kano, da Malamai, da wakilcin Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano, da kuma jami'an hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi, NDLEA, sai Ƙungiyoyi da Kwamitocin ci gaban al'umma da na tsaro, da Ƴan Bijilante da dai sauransu.



